<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>346</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) A cikin farko Allah ya
 Halitta sama da ƙasa.
 Ta wurin ikon maganarsa
 Duniya da kome sun zama.

[V2]
 KORUS
 Mai iko, Mai iko
 Allah ne Mai ikon kome,
 Mai iko, Mai iko
 Allah ne, Mai ikon dukan kome.

[V3]
 2) Ҡasa fa duka wofi ce
 Duhu ya rufe ruwaye.
 Rana ta fari Allah ya ce
 Bari haske shi kasance.
 Korus

[V4]
 3) Rana ta biyu Allah ya ce
 Bari sarari ya kasance,
 Kuma ya raba ruwaye
 Haka ya zama gaba dai.
 Korus

[V5]
 4) Rana ta uku tekuna
 Sun tattaru wari ɗaya.
 Ciyawa da itatuwa
 Kowane masu bada ƙwaya.
 Korus

[V6]
 5) Rana ta huɗu an gani
 Can cikin sama haskoki
 Bisa duniya su yi mulki
 Rana da wata da tamrari.
 Korus

[V7]
 6) Rana ta biyar Allah ya ce
 Kifi su cika ruwaye,
 Tsuntsayen sama su yalwaita,
 Su haifu har duniya ta cika.
 Korus

[V8]
 7) Rana ta shidda bisashe
 Ya yi su, masu-rarrafe
 Mutum da mananinsa ne
 Haka ya gam aikin ne.
 Korus

[V9]
 8) Rana ta bakwai Allah fa
 Ya huta daga aikinsa
 Haka mu kuma ƴayansa
 Mu huta rana guda kuwa.
 Korus</lyrics>
<title>A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa LW346</title>
</song>